2 Mayu 2020 - 03:52
Iran Ta Lashi Takobin Mayar Da Martani Idan Har Amurka Ta Keta Yankinta Na Ruwa

Jamhuriyar musulinci ta Iran ta ce za ta mayar da martini mai tsauri idan har jiragen ruwan Amurka suka keta yankin ruwan kasar yayin da suke wucewa.

(ABNA24.com) Kakakin rundunar sojin Iran, Abolfazl Shekarchi na mai sukar Amurka ne bisa abun da ya kira "tayar da hankali" a mashigin tekun Fasha.

M. Shekarchi, ya kuma yi watsi da barazanar shugaba Trump ta baya bayan nan dake da nufin jan hankalin jama'a, gabanin zaben shugaban kasar.

A makon da ya gabata ne, Donald Trump ya ce ya ba rundunar sojin ruwan kasar umarnin harbin jiragen tsaron ruwan Iran dake matsawa jiragen Amurka a mashigin tekun.

A cewar Abolfazl Shekarchi, ya kamata Amurkawa su sani cewa, idan suka yi wani yunkurin da ya keta yankin ruwan kasar ko muradun al'ummarta, to kasarsa za ta mayar da martani fiye da wanda suka gani a baya.



/129